IQNA

Karbala; Gasar Kur'ani Mai tsarki Ta Matan Iraki

17:20 - July 21, 2016
Lambar Labari: 3480632
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wata gasar kur'ani mai tsarki ta matan Iraki a birnin karbala mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, za a gudanar da wannan gasar ne tare da haklartar mata daga sassa na kasar a karkashin shirin cibiyar Nur Zahra (SA) wanda zai hada da hardar kur'ani baki daya, da kuma hardar izihi 20 na kur'ani.

Shirin dai an agudanar da shi a lokuta daban-daban, amma na shekarar ban azai sha banban da sauran wadanda suka gabata, kasantuwar cewa shirin yana dauke bangarori na aka kara na gasar.

Daga cikina abubuwan da shirin zai kunsa, akwai hardar kur'ani baki daya, sai kuma harda ta wasu bangarori na kur'ani, bayan kuma akwai karatu da kuma ilimin hukuncin karatu.

Akwai adadi mai yawa na daruruwan mata mahardata da makaranta da suka rijistar sunayensu domin halartar wannans hirin wanda ya kebanci mata kawai, wanda kuma ake ganin zai kara karfafa gwiwar sauran mata wajen mayar da hankali ga lamrin kur'ani mai tsarki.

captcha