Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa
ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tashar talabijin
ta Almanar ta bayar da rahoton cewa, a ci gab ada daukar matakan nuna wariya da
bangarancin banbancin mazhaba da masarautar Bahrain take a kan mafi rinjayen
al'ummar kasar,a yau sun hana a gudanar da sallar Juma'a a yankin diraz a
babban masallacin Imam Sadiq (AS) babban massalaci mafi girma ayankin
baki daya.
Wannan mataki dai ya zo a hankoron da masarautar mulkin kama karya ta kasar da ke samun goyon baya daga kasashen Amurka da Birtaniya gami da Saudiyya take yi ne na murkushe mabiya mazhabar shi'a akasar, wadanda su ne fiye da kashi 85% na al'ummar kasar baki daya, yayin da mahukuntan kasar suke daga cikin 'yan sunna da ake lassafa a su a cikin 'yan tsiraru, a kasar.
Tun kimanin kwanaki 33 da suka gabata ne masarautar ta sanar da janye izinin zama dan kasa daga kan babban malamin addini mafi tasiri a kasar a kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim, inda kuma suke neman kama shi tun alokacin, amma hakan bai yiwuwa ba, saboda al'ummar kasar ba su taba barin hakan ta faru ba, da kuma masaniyar da mahukuntan kasar suke da ita kan cewa, taba Ayatollah Sheikh Kasim yana daidai da kawo karshen mulkinsu ne a kasar baki daya.