
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Pulse cewa, Muhammad Ibrahim Zakzaky a cikin wani sako da ya aike zuwa ga shugaba Buhari da sairan duk wani fada a ji a Najeriya, ya bukaci da a taimaka ma mahaifinsa kan halin da yake ciki na matsalar iduna.
Muhammad Zakzaky ya ce suna cikin damuwa matuka dangane da halin da mahaifinsu yake ciki, musamman ma ganin cewa idonsa guda a halin yanzu baya gani, kuma idan ba a bas hi kulawar da ta dace ba zai iya rasa daya idonsa.
Ya kara da cewa baya ga matsalar idonsa, yanzu haka ma jikinsa yana yin rauni ta yadda wani bangarensa baya aiki sosai, kuma abin ban takaici shi ne babu wani tsayayyen likita da yake kula da shi.
Muhammad Ibrahim ya kara da cewa wannan nauyi da ya rataya kan duk wanda yake da sauran karama da ‘yan adamtaka a cikin zuciyarsa, domin kuwa babban abin da mahaifinsu ke bukata shi ne kulawa ta fuskar lafiya.
Tun bayan da mahukuntan Najeriya suka kama Sheikh Zakzaky bayan kisan kiyashin da aka yi a Zaria da sunan tare wa kwamandan sojojin Najeriya hanya, har yanzu ba a san halin da kusan mutane dubu daya suke ciki ba, wadanda ake zargin sojojin sun kasha su tare da bizne gawawwakinsu.