IQNA

An Janye Dokar Hana Sa Hijabi Ga ‘Yan Makaranta A Najeriya

23:34 - July 23, 2016
Lambar Labari: 3480639
An Janye Dokar Hana Sa Hijabi Ga ‘Yan Makaranta A Najeriya
Bangaren kasa da kasa, kotun daukaka kara a jahar Lagos da ke tarayyar najeriya ta janye dokar hana saka hijabi ga daliban makarantun sakandare.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na world Bulletin cewa, a ranar Alhamis da ta gabata kotun daukaka kara a jahar Lagos da ke tarayyar najeriya ta janye dokar hana saka hijabi ga daliban makarantun sakandare da hukumomin jahar suka kafa.

Wannan hukunci da ta kotun ta yanke ya zo ne bayan kwashe shekara guda a jere ana ta bin kadun wannan batu a shar’ance, inda daga karshe saboda rashin dalilai daga bangaren mahuknta kotun ta yanke hukuncinta na karshe kan batun.

A shekarar 2014 da ta gabata ce dai mahukuntan jahar Lagos suka sanar da kafa dokar hana yan mata daliban sakandare saka hijabin musluci bisa hujjoji na tsaro, lamarin da ya fuskanci kakakusar suka daga musulmin jahar da kuma kngiyoyin farar hula.

Har yanzu dai mahukuntan jahar ta Lagos bas u ce komai kan wannan hukunci na kotun daukaka kara ta jahar ta yanke ba, amma dai jama’a a koina a cikin fadin jahar suna ta shewa da nuna murnarsu kan wannan hukuncin da kotun ta yanke.

3516914


captcha