Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na Nailain cewa, an samu kwafin kur'anin ne dauke
da kura-kurai masu yawa, wadanda za su kawo matsala matuka.
Bayanin ya ce cibiyar ta buga wadannan kur'anai ta samu wata takardar lasisi ne ta jabu daga wata kasar larabawa domin buga kur'anai da sunan cewa ta samu lasisin ne daga cibiyar Azahar ta kasar Masar.
Yanzu haka dai an kwace dukaknin kurnan da suka shiga kasuwa da ma wadanda suka shiga hannun mutane, a daidai okacin da ake ci gaba da bayar da sanarwa a koina a cikin fadain kasar ta Sudan kan cewa, duk wanda ya samu wannan kwafin kur'ani to ya gagaguta kawo shi.
Daga cikin irin kura-kuran da aka samu har da cire wasu daga cikin shafukan kur'ani da ayoyin da ke cikinsu, kamar yadda kuma aka cire wasu kanan surori, haka nan kuma an saka wasu abubuwan da bas u ciki, wanda hakan yana tattare da babban hadari na canja tsarin kur'ani da kuma nakasta shi.
Jama'a da dama dai sun bayar da hadin kai ci gaba da tattaro wadannan kur'anai da aka buga kan kure, ko kuma ta hanyar yaudara domin cutar da musulmi da addainin muslunci.