IQNA

Kur’anin Rubutun Hannu Da Ya Fi Karanta A Duniya A Ina Yake?

23:40 - July 25, 2016
Lambar Labari: 3480644
Bangaren kasa da kasa, kur’anin da ya fi karanta na rubtun hannun a duniya shi ne wanda tarihinsa ke komawa zuwa shekra ta 1100 wato fiye da shekaro 300 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisrawi cewa, tsawon wannan kur’ani baki daya bai fi CM4.1 b, kuma shi ne ya zuwa yanzu mafi karantar kur’ani rubutun hannu.

Shugaban cibiyar da ke kula da harkokin adana kayan tarihi a kasar Yemen ya bayyana cewa, wannan kur’ani ya jima a hannun wannan cibiya, kuma an same shi ne akasar.

Ya kara da cewa har yanzu ba za a iya tntance ko zuwa wane mutum ne wannan kur’ani ke komawa ba, amma dai abin da aka tabbatar da cewa shi ne kur’ani rubutn hannu mafi karanta a duniya a halin yanzu, duk da tsawon shearunsa.

Dangane da yadda ake kula da shi kuma ya bayyana cewa, domin kada takardunsa su lalace, ana kula da shi yadda ya kamata a cikin tsawon wadannan daruruwan shekaru.

Yanzu haka dai za a iya ganin kur’anin da shafukansa da kuma rubutnsa ba tare da wata matsala ba, kamar yadda har yanzu takardunsa na asaline har da bangyensa.

3517671

captcha