Kamfanin dilalncin labaran iqna ya
nakalto daga shafin sadarwa na Press TV cewa, daga cikin malaman da aka kama
har da Sayyid Yasim Musawi da kuma Sheikh Jasim Alkhayyat, bisa hujjar cewa sun
halarci taron nuna goyon baya ga Ayatollah Isa Kasim, babban malamin addini na
kasar, wanda masarautar kasar ta janye izinin zama dan kasa daga gare shi.
Haka nan kum rahoton ya kara da cewa jami’an tsaon masarautar ta Bahrain sun kai farmaki kan gidan Sheikh Aziz Alkhadran, daya daha cikin manyan malaman addini na kasar, inda shi ma suka kama shi, bisa hujjar cewa yana sukar salon siyasar masarautar kasar.
Masarautar mulkin mulukiya ta Bahrain ta fara daukar matakan takura al’umar kasar ne tun daga shekara ta 2011, inda suka bukaci a kamanta adalci a cikin rabon arzikin kasar, maimakon mayar da dukiyar kasa da al’ummarta da siyasarta duka mallakin sarki da iyalansa.
A baya-bayan nan dai masarautar ta Bahrain ta dauki matakin da da dama daga cikin al’ummar kasar ke kallonsa a matsayin ta debo ruwan da za a dafa ta da shi, inda ta janye izinin zama dan kasa daga Ayatollah Isa Kasim, babban malamin addini wanda ya fi kowa tasiri a cikin zukatan mafi yawan al’ummar kasar.