
A wannan talata Kotun hukunta manya laifuka ta kasar Bahrain ta sanar da fara sauraren karan Shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahren Shekh Isa Kasim wanda ake zarki da laifin tunzura Al'umma wajen yiwa Gwamnati tawaye a gobe Laraba.
Kafin wannan sanarwa Al'ummar yankin Adderaz na birnin Manama sun taru a gaban kotun domin neman kotun da ta sanya ranar sauraren karar na shekh Isa Kasim.
Gwamnatin ta Bahrain na ci gaba da kamen manya-manyen malimai mabiya mazhabar Shi'a da kuma dukkanin wani Dan siyasa ko kuma babban mutun dake adawa da siyasar ta.
A bangare guda, kungiyoyin kasar dake adawa da bakar siyasar masarautar Ali khalifa dake zaune a kasashen waje sun bukaci kungiyoyin kasa da da kasa da kasashen masu 'yanci na Duniya da su dauki matakin gaggawa domin kawo goyon bayansu ga Al'ummar kasar Bahrain, inda suka Ayyana ranar juma'a ashirin da tara ga wannan wata na Yuli shekarar dubu biyu da sha shida a matsayin ranar goyon bayan Al'ummar kasar Bahrain.
Ko shakka babu wannan mataki na wawanci da rashin tunani da hangen nesa da sarki Bahrain ya nuna a kan batun wannan babban malami, ga dukkanin alamu zai zama shi ne digon ban a karshen mulkinsa.
Yanzu haka dai al'ummar kasar suna cikin shirin fuskatar kowane irin mataki da mahukuntan mulkin kama karya na kasar za su iya dauka a kan wannan malami wanda ya fi kowa tasiri a cikin zukatan al'ummar kasar.