IQNA

Za A Gina Cibiyar Hardar Kur'ani Ta Zamani A Masar

23:52 - July 26, 2016
Lambar Labari: 3480648
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar masar ta amince da gina wani wuri na musamman domin hardar kur'ani a gundumar Suis.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alarabiyyah News cewa, a cikin wannan makon ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar masar ta amince da gina bababr cibiyar hardar kur'ani ta zamani a cikin lardin Suis da ke arewacin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an kammala dukkanin shirin da ya kamata domin fara wannan aiki, wanda zai zama shi ne irinsa na farko da za a gudanar a kasar ta Masar, da nufin kuma ya zama mafin ci gaba ga ayyukan kur'ani mai tsarki.

Wannan cibiya dai za ta hada da ajujuwa da kuma dakunan karatu, gami da masallaci da wuraren hutawa gami da wuraren shiga yanar gizo domin yin binck kna lamurra da suka danganci kur'ani mai tsarki.

Shi dai tsarin ana ganin zai taimaka ma masu son hardace kur'ani su yi saurin hardace shi cikin kankanin lokaci, kuma ta hanya da zai zauna akansu, domin kuwa za a yi amfani da hanyoyi na koyarwa na musamman.

Jama a da dama sun nun gamsuwarsu da shirin, da kuma yin fatan Allah yasa ya yi nasara kuma y adore.

3517930

captcha