Kamfanin dillancin labaran iqna ya
bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada
aladun muslunci cewa, a cikin wannan makon ne za a fara gudanar da wani shiri
na kur'ani mai tsarkia kasar Senegal,
wanda aka gayyaci Iran a matsayin bakin karamci a taron.
Bayanin ya ce wannan taro ana gudanar ad shi a kowace sheakara, wanda shugaban kasar ke daukar nauyinsa, tare da wasu daga cikin manyan malaman darikun sufaye na kasar.
Tawagar ofishin jakadancin Iran da kuam ofishin yada al'adun muslunci na Iran a Dakar ne aka gayyata awajen taron, wanda zai gudana aranar asabar mai zuwa, kuma an gayyaci mutane fiye da dubu uku da za su halarci taron, da suka hada da malamai da kuma masana daga sasasn kasar.
Daga cikin abubuwan da za a yi har da karatun kur'ani mai tsarki, daga makarantun sufaye na kasar, sai kuma baje koli na kayan tarihi da ilimi da suka hada da littafai na rubutun hannu da suka jima, da sauran kayayyakin na al'adun muslunci a kasar.