Kamfanin dillancin labaran Iqn aya
habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Naba cewa, a jiya
wasu jami’an tsaron kasar Masar sun dakile wani yunkurin satar wani dadden kur’ani
a kasar daga gidan wani mtum mai suna Muhammad Mu’ayyid Al-iraqi dan asalin
Iraki mai shekaru 55 mazaunin kasar ta Masar.
Bayanin ya ci gaba da cewa an samu bayanan sirri ne dangane da yadda yake shirin ficewa daga kasar da wannan kur’ani mai tsohon tarihi, amm bayan gudanar da bincike a cikin gidansa tare da wani abokinsa mai suna Ibrahim Ahmad Kurdi dan shekaru 47 an gano wannan kur’ani.
Wannan bincike dai y faru ne bayan sakamakon rahoton da aka samu na sace wannan kwafin kur’ani daga wani dakin karatu na tarihi, wanda kuma jami’an tsaro sun samu bayani ta hanyar abokan mutumin.
An samu wannan kur’anin wanda aka rubuta shit un cikin shekara ta 1258 a cikin wata takatarda mai fadin CM 23 a cikin 11, yayin da kuma fadi da tsawon takardun kur’ani ya kai CM 23 a cikin 16 kamar dai yadda jami’an tsaron suka tabbatar.