IQNA

Kotun Kuwait Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 14 A Kan Wani Dan Majalisar Kasar

23:48 - July 28, 2016
Lambar Labari: 3480655
Kotun Kuwait Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 14 A Kan Wani Dan Majalisar Kasar
Bangaren kasa da kasa, Kotun kasar Kuwait ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 da rabi a kan dan majalisar dokokin kasar Abdulhamid dashti saboda sukar gwamnatin saudiyya da ya yi kan kashe fararen hula da take yi a kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, Tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton cewa, kotun masarautar ta kasar Kuwait ta yanke hukuncin daurin shekaru goma 11 a kan Abdulhamid dashti ne saboda sukar masarautar Saudiyya da ya yi kan kai hare-haren da take yi kan kasar larabawa ta Yemen da ke makftaka da ita, tare da kashi dubban fararen hula.

Haka nan kuma kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru uku da rabi a kansa sakamakon nuna rashin amincewa da cin zarafin 'yan adawa da kuma masu fafutukar kare hakkin bil adama da malaman addini da masarautar Bahrain ke yi, saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba.

Kotun ta ce bisa wadannan dalilai yta yanke hukunci a kansa bayan cire masa kariya, duk kuwa da cewa a halin yanzu baya acikin kasar, amma hukuncin na nan na jiransa a duk lokacin da ya dawo.

Abdulhamid dashti baya kasancewarsa dan majaliar dokokia Kuwait, shi ne kuma shugaban cibiyar kare hakkin bil adama mai zaman kanta a kasar Kuwait.

3518400

captcha