IQNA

Abin Bakin Ciki Ne Da Takaici Yadda Saudiyya Ta Kulla Kawance Da Isra’ila

23:30 - July 29, 2016
Lambar Labari: 3480657
Bangaren kasa da kasa, Dangane da batun Palastinu da wurare masu tsarki na musulmi babu maganar kawaici ko noke-noke dole ne masana da malamai su fito su bayyana rashin halascin hakan ko a Saudiyyah ne ko Jordan ko Masar ko Pakistan, da sauransu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar Almanar cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah yayi kakkausar suka ga kokarin da kasar Saudiyya take yi na kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila da kulla alaka da ita, yana mai kiran al'ummar musulmi da su yi Allah wadai da duk wani kokari na kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila da yin watsi da matsalar Palastinu.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne jawabin da yayi dazu-dazun nan wajen bikin tunawa da daya daga cikin kwamandojin kungiyar ta Hizbullah Ismail Ahmad Zahri, wanda ya rasu a makon da ya wuce sakamakon fama da cutar 'cancer' da yayi fama da ita inda yace kasar Saudiyyan tana kokarin mayar sanar da kulla alakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila a fili ne ba tare da ma ta sami wani abu ba ko kuma ba tare da wani amfani da al'ummar Palastinu za su samu ba.

Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa abin bakin ciki ne yadda wasu kasashen larabawa suka yi watsi da matsalar Palastinu da mai she shi ba a bakin komai ba.

A wani bangare na jawabin nasa Sayyid Hasan Nasrallah yayi kakkausar suka ga akidar wahabiyanci da kasar Saudiyya take yadawa a duniyar musulmi wanda shi ne ummul aba'isin din dukkanin ayyukan ta'addancin da wasu kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Da'esh da sauransu suke yi da sunan Musulunci.

Dangane da kasar Bahrain kuwa, Sayyid Nasrallah ya soke lamirin gwamnatin Al Khalifa na kasar da take samun goyon bayan Saudiyya dangane da irin matakin da take dauka na takurawa Shehin malamin kasar Sheikh Isa Qasim.

Yayin da ya koma kan kwamandan dakarun kungiyar da ya rasu din kuwa, Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar Ismail Ahmad Zahri ya kasance daga cikin kwamandojin dakarun kungiyar Hizbullah din da suka taka gagarumar rawa yayin yakin shekara ta 2006 da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar kan kasar Labanon inda ta sha kashi a hannun dakarun kungiyar ta Hizbullah.

3518625

captcha