IQNA

Kyautar Da Zarif Ya Samu A Kasar Guinea

23:45 - July 30, 2016
Lambar Labari: 3480661
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin mabiya mazhabar iyalan gidan manzo sun bayar da kyautuka na musamman ga ministan harkokin wajen kasar Iran a ziyararsa a Guinea.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafi ma'aikatar harkokin wajen Iran cewa, ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif ya kammala ziyarar aiki da ya gudanar a yammacin nahiyar Afirka, wadda yafa tun daga daren Lahadin da ta ta gabata.

A ranar Laraba, Zarif ya isa birnin Conakry fadar mulkin kasar Guinea Conakry, inda a can ma ya gudanar da tattaunawa tare da manyan jami'an kasar da suka hada da shugaban kasar Alfa Conde, da kuma firayi ministan kasar Mamadi Yula, da kuma shugaban majalisa da kuma ministocin harkokin waje da na tattalin arzikin kasar.

Babban abin da ziyarar ta Zarif ya mayar da hankali a kansa dai shi ne batun kara bunkasa alaka ta diplomasiyya da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Iran da kasashen yammacin nahiyar Afirka, sai kuma batun noma da hanyoyin yaki da ayyukan ta'addanci, da kuma yadda dukkanin bangarorin za su iya yin aiki tare domin fuskantar wannan hadari.

Zarif wanda a yau ne zai iso gida bayan kammala wannan ziyara, ya fadi a daren jiya a birnin bamako cewa, ziyarr tasa ta yi nasara matuka, kuma hakan ya bayar da damar bude wasu shafuka na kara fadada alaka tsakanin Iran da wadannan kasashe masu matukar muhimmanci a nahiyar Afirka.

captcha