IQNA

Masarautar Bahrain Ta Kame Shugaban majalisar Malaman Kasar

23:47 - July 30, 2016
Lambar Labari: 3480662
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bahrain sun kame shugaban majalisar malaamna ddinin muslunci ta kasar Sayyid Majid Mash'al, ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba.
Tuna jiya ne dai mahukuntan kasar ta Bahrain suka bayar da umarnin kame Sayyid mash'al, inda jami'an tsaroa cikin kayan sarki suka kai farmaki akn gudansa a cikinsa iyalansa, da suka yi awon gaba da shi da sunan za su gudanar da bincike da kuma yi masa tambayoyi, daga nan kuma sai suka rike shi.

Wannan dai ba shi karon farko da masarautar kama karya ta Bahrain ta kame malamin ba, domin kuwa ko a shejkarar da ta gabata an kame shi da sunan zai amsa tambayoyi, kafin daga bisani aka sake shi.

Masarautar Bahrain dai ta fara daukar wannan mataki akna malan adini musamamn mabiya mazhabar shi'a ne a cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan, da nufin murkushe su da kuma mayar ad su saniyar ware baki daya.

Wannan mataki yana zuwa ne bayan da masarautar ta kasa fitar da bababn malmin addini na kasar Ayatollah Sheikh Isa Qasem wanda ta jane izinin zama dan kasa a kansa, kuma ta kiraye shi zuwa kotu, amma dai ya yi watsi da kiran, kuma bai halarta ba.

3518679

captcha