Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin Rased cewa, sojin Iraki sun samu nasarar
halaka babban mai bai wa kungiyar 'yan ta'addan Takfiriyyah Wahabiyyah ta Daesh
fatawa a yankin Sherkat da ke cikin
gundumar Salahuddin da ke arewacin kasar tare da dukkanin masu tsaron lafiyarsa.
Bayanin aya ci gaba da cewa dakarun Irakin sun kaddamar da hari ne ta sama a maboyarsa, bayan samun cikakkun bayanai kan inda yake, wanda kuma an kaddamar da harin cikin nasara tare da halaka shi.
A cikin shekara ta 2014 ne mutumin ya shigo cikin kasar Iraki daga kasar Saudiyya, kuma ya zama shi ne yake baiwa yan ta'addan fatawa kan kisan kiyashin da suke wa musulmi tare da kafurta su.
Yanzu haka dai rundunar sojin Iraki tana ci gaba da nausawa acikin sauran yankunan da ke hannun daesh da nufin karbe su, kuma an asamun gagarumar nasara, bayan da tsoro ya shiga cikinzukatan 'yan ta'addan.