IQNA

Fitaccen Makarancin Kur’ani Na Kasar Iran A Senegal

22:12 - July 31, 2016
Lambar Labari: 3480664
Bangaren kasa da kasa, Majid Zakilu fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran a wurin babban taron kur’ani a masallacin Dakar na kasar Senegal.
Kamfanin dillancin labaran iqa ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, Majid zalilu ya tafi kasar ta Senegal ne bayan da ya samu takardar gayyata daga babbar cibiyar makarantun musulunci ta kasar.

Ya gabatar da karatun wasu daga cikin ayoyin kur’ani mai tsarki a wurin taron wanda ake gudanarwa a masallacin Dakar tare da halartar dubban musulmi, kamar yadda kuma Sayyid Hassan Esmati karamin jakadan Iran a kasa ya samu halrtar wurin.

Zakilu ya mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka shirya wannan taro mai albarka, tare da yin fatan kur’ani mai tsarki ya zama abin da zai kara hada kan musulmi a duniya baki daya.

Haka nan kuma ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki tare da dukkanin bangarorin da suke gudanar da harkokin kur’ani a kasar ta Senegal domin raya wannan littafi mai tsarki.

3519030

captcha