Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin Mir’at Bahrain cewa, cibiyar kare hakkin
bila dama ta kasar ta Bahrain ta ce hakika kame Sayyid Majid Mash’al shugaban
majalisar malaman kasar abu ne da ya sanawa dukkanin dokokin kasar.
Bayanin ya ce Sayyid Majid Mash’al na daga cikin fitattun malaman kasar Bahrain masu son zaman lafiya, tare da yin kira akowane lokaci zuwa ga tattauna domin samun fahimtar juna tsakaninsu da bngaren hukuma, amma yau gas hi hukumar ta kame shi, lamarin da ke nuni da cewa ba ta son zaman lafiya.
Wannan mataki dai ya zo sakamakon yadda Sayyid Mash’aya kasance a sahun gaba wajen nuna cikaken goyon baya ga babban malamin addinin muslunci na kasar Ayatollah Isa Kasim, duk kuwa da cewa shi dama daya ne ne daga cikin manyan almajiransa.
Masarautar mulkin kama karya ta iyalan gidan khalifa ta kudiri aniyar kawo karsehn dukkanin mabiya amzhabar shi’a akasar Bahrain wadanda su ne asalin yan kasar kuma addain yah aura kasha tamanin da biyar cikin dari.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama a koina cikin duniya suna ta yin Allawadai da akakusar murya dangane da wannan mataki, da kuma yadda kasashen duniya musamman na turai suka yi gum da bakunansu kan wannan ta’asa.