Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da
rahoton cewa, kafofin yada labarai na kasar Trkiya sun bayar da muhimamnci
dangane da jawabin jagora na baya-bayan nan.
Daga cikin shafukan Turkiya da ska nakalto bayanin har shafin Star, da kuma Hurriyat, sai kuma jaridun Titer da kuma elri sai kuma shafin A24 da sauransu, musamman ma dangane da zargin da jagoran yayi na cewa Amrka tana da hannu a ynkurin juyin mulki a kasar ta Turkiya
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi jawabin nasa ne a wata ganawa da yayi a yau din nan Litinin da dubun dubatan mutanen da suka fito daga jihohi daban-daban na Iran inda ya ce yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma ya tabbatar rashin amfanin tattaunawa da kulla yarjejeniyar da Amurka, da kuma cewa lalle ita ba abar yarda ba ce, kamar yadda kuma ya tabbatar da cewa hanya guda kawai ta tabbatar da ci gaban kasa ita ce dogaro da kai da kuma irin karfin da ake da shi a cikin gida, ba wai makiyan da a kullum ba abin da suka sa a gaba in banda kafar ungulu da duk wani kokari na ci gaban kasar ba.
Yayin da kuma yake magana kan kokarin da kasar Saudiyya ta ke yi na kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila, Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan a matsayin babban ha'inci kana kuma cin kafar al'ummar musulmi, daga nan kuma sai ya ce: Ko shakka babu wannan kulla alakar babban kuskure da kuma cin amana ne.
Haka nan kuma yayin da ya koma kan abin da ke faruwa a kasar Bahrain kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce amfani da karfin soji da wasu kasashen waje suke yi a kan al'ummar Bahrain wani kokari ne na rufe bakin al'ummar kasar da kuma tilasta musu abin da ba sa so.