IQNA

An Kammala Zaman Bayar Da Horo Na Kur’ani A Kasar Uganda

23:01 - August 06, 2016
Lambar Labari: 3480682
Bangaren kasa da kasa, an kammala wani zaman bayar da horo kan kur’ani mai tsarki a kasar Uganda.

Kmafanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa an kammala wani taro na bayar da horo kan ilmomin kur’ani mai tsarki a kasar Uganda, wanda kwalejin jami’ar Amustafa SAW) ta dauki nauyin shiryawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman abubuwan da wannan taro na bayar da horo ya mayar da hankali a kansu akwai ilimin zamantakewa da kuma tarihin muslunci gami da sanin zamantakewa a muslunce da kuma kyawawan dabiu, sai kuma tarihin Sayyida Zahra (AS).

Ali Bakhtiyari shi ne shugaban ofishin kula da harkokin addini da al’adu na kasar Irana Uganda, ya bayar da darussa a jin maza kan al’adun muslunci da kuma zamantakewa a muslunce, kuma yana bayar da darasin na tsawon sa’oi 4 a kowace rana.

A taron rufe wannan horo an bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin mahalarta na littafai da kuma kudade gami da abubuwa da za su taimaka musu domin ci gaba da neman ilimin addini.

3520522

captcha