IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai da Yunkurin Kashe Tsohon Muftin Masar

23:03 - August 06, 2016
Lambar Labari: 3480683
Bangaren kasa da kasa, Shauki Allam ya sanar da cewa yunkurin kashe Ali Juma tsohon maia bayar da fatawa na Masar aikine na ta’addanci.

Kmafanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Misr yaum cewa, malaman kasar sun fitar da wani bayani na bai daya da ke yin Allah wadai da kakkausar murya kan yunkurin kashe tsohon mai bayar da fatawa na kasar.

Ma'aikatar cikin gidan kasar Masar ta sanar da cewa tsohon muftin kasar Ali Jum'ah ya tsallake rijiya da baya a kokarin kashe shi da aka yi a wani masallaci a birnin Alkahira da yake jagorantar sallar Juma'a a wajen.

Kamfanin dillancin labaran ya ce ma'aikatar cikin gidan Masar din cikin wannan sanarwa da ta fitar ta ce wasu mutane biyu da suke kan babur ne suka buda wa Sheikh Ali Juma'ah wuta a lokacin da yake kokarin shiga masallacin da yake bada sallar Juma'ah a jiya Juma'ar.

Rahotannin sun ce babu wani abin da ya sami Shehin malamin sai dai daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ya sami rauni, mahalan biyu dai sun tsere ba tare da an kama su ba.

Sheikh Ali Juma'ah dan shekaru sattin da hudu a duniya ya ya kasance muftin kasar ta Masar ne daga shekara ta dubu biyu da uku zuwa ta dub biyu da sha uku.

Wata kungiyar mai suna Hasam ta sanar da cewa ita ce ta kai wannan harin.

3520439

captcha