IQNA

Masarautar Bahrain Ta Kame Manyan Malamai 3 Na Kasar

23:05 - August 06, 2016
Lambar Labari: 3480684
Bangaren kasa da kasa, masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta kame manyan malaman addini na kasar guda uku sabododa dalilai na siyasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na shafaqna cewa, daga cikin malaman da aka kama har sheikh Muhsin Alguraifi, da sheikh Fadil Zaki, da kuma sheikh Ali Naji Almuhli.

Wannan mataki yana zuwa ne a daidai lokacin da masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ke ci gaba da yunkurin ganin cewa bisa dalilai na siyasa da kuma banbancin mazhaba ta mayar da mabiya mazhabar shi’a na kasar saniyar ware a cikin dukkanin lamurra kasar.

Kafin wannan lokacin dai masarautar ta kame Sayyid majid Masha’al shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar, bisa hujjar cewa yana goyon babban malamin addini na kasar wanda baya dasawa da wannan masarauta.

A cikin shekara ta 2014 ce masarautar ta sanar da soke majalisar malaman addini ta kasar kasantuwar cewa akasarinsu mabiya mazhabar shi’a ne, ba tare da yin la’akari da cewa fiye da kashi tamanin biyar cikin dari na mutanen kasar mabiya mazhabar shi’a ne ba.

3520601

captcha