IQNA

An Kammala Wani Horo Kur'ani Mai Tsarki A Senegal

23:54 - August 07, 2016
Lambar Labari: 3480686
Bangaren kasa da kasa, an kammala wani shiri na bayar da horo kan kur'ani mai tsarki wanda aka gudanar a cibiyar Jami'ar Almustafa (SAW) da ke Senegal.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun musunci cewa, an gudanar da zaman taron bayar da horon wanda shi ne irinsa na farko a cikin nasara, tare da halartar malaman kur'ani 23 daga larduna 14 na kasar ta Senegal a ginin cibiyar ta jami'ar Almustafa (S).

An dai koyar da abubuwa da dama da suka danganci kur'ani kama da kira'a da salo daban-daban, da kuma kayutata tajwidi da wasu hukunce-hukunce na karatu.

Sayyid Hassan Esmati shugaban ofishin kula da harkokin al'adu na kasar Iran a kasar ta Senegal da kuma Sheikh Mustafa Lu, daya daga cikin manyan malaman addini na kasar duk sun halarci wurin rufe wannan taro na bayar da horo.

Masana da malamai na kasar ta Senegal da suka halarci wurin sun yaba matuka da yadda kasar Iran tak ebayar da muhimmanci wajen yada ilmomin kur'ani mai tsarki a kasar tare da halartar makaranta daga kasar a wannan taro.

3520800

captcha