Bayanin ya ce an gabatar da wakokin yabo ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma limaman shiriya daga cikin iyalansa, kamar yadda wani makaranci daga kasar Iran ya gabatar da karatun kur'ani mai tsarki a wurin.
Wannan taro ya samu halartar Mardiyyah Afkham jakadiyar kasar Iran a Malaysia da kuma Ali Akabar Ziya'i shugaban ofishin karamin jakadancin Iran a Malaysia, gami da wasu daga cikin masana da malaman jami'oi na kasar, wadanda suka halarci domin karuwa.