Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren cewa, a wata tafiya da wata tawaga ta yi zuwa yammacin nahiyar Afirka musamman a kauyukan Sawafi na Senegal da kuma Nyama na Saliyo an bukaci taimako ta fuskar addini.
Bauanin ya ci gaba da cewa al’ummomin wadannan kauyuka biyu mutane masu kula da addini matuka, kuma mafi yawansu kimanin kasha 90 cikin dari sunabin mazhabobi ne na sunna haka nan kuma yan darika ne na sufaye.
Daga cikin irin abubuwan da suka bukata daga wannan hubbare mai tsarki da kwafin kur’anai da kuma sauran littafai na addini, musamman ganin cewa suna da bukatuwa matuka, amma babu hanyoyin da za su same su kamar yadda suke bukata.
Yanzu haka dai wanann hubbare ya samu wannan sako, kuma masu tafiyar da shi sun sha alwashin ganin an aike da dukkanin abubuwan da aka bukata awadannan kauyuka biyu, kamar yadda kuma za a ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka na alkhairia yankna daban-daban na yammacin nahiyar Afirka.