IQNA

Daula Da Addini A Mahangar Imam Ridha (AS) A Radiyon Senegal

23:50 - August 17, 2016
Lambar Labari: 3480718
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani shirin radiyon Senegal dangane da mahangar Imam Ridha (AS) kan addini da kuma daula.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada aladun muslunci cewa, a daidai lokacin maulidin Imam Ridha (AS) an gudanar da shiri na musammana gidan radiyon Senegal a lardin Fatika na wanan kasa.

Sheikh Talibu Lu shi ne ya jagoracin shirin tare da yin hira da Sayyid Hassan Ismati shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal, wamnda ya yi bayani kan matsayin Imam Ridha (AS) tare da bayyana cewa hakika al'ummar wanann kasa suna son iyalan gidan manzo, amma suna karancin masaniya kan hakikanin wadannan tsarkakan mutane.

Wannan dais hi ne karo na uku da ake gudanar da shiri maulidin Imam Ridha (AS) a kasar ta Senegal, tare da wayr da kan jama'a dangane da matsayin iyalan gidan manzo.

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna senegal imam ridha fatika shiri maulidin kasa
captcha