Wanann shiri dai ya hada da gudanar da wasu canje-canje a cikin birnin Quds, tare da rushe wasu wurare da kuma gina wasu, daga cikin wuraren da za a rusa bisa wanann shiri na yahudawa kuwa har da masallacin Quds, da wasu daga cikin wurare masu tsarki na musulmi da kiristoci da ke birnin, kamar yadda hakan zai hada da rusa dubban gidajen Palastinawa.
Rahoton ya ce yanzu haka an kammala zanen birnin yadda zai kasance bayan kammala aiwatar da shirin baki daya, wanda zai dauki shekaru akalla uku a nan gaba, tare da lakume makudaden kudade, manyan kamfanonin zane guda uku na duniya ne da suka hada har da na Jamus, suka gudanar da aikin zanen taswirar.