IQNA

Jami’an Tsaron Saudiyya Sun Kame Malamin Shi’a Biyu A Makkah

11:29 - September 03, 2016
Lambar Labari: 3480759
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Saudiyyah sun kame wasu malaman shi’a biyu da suka fio daga yankin Qatif a garin Makka.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, jami’an tsaron gwamnatin Saudiyyah sun kame sheikh Fahmi Zainuddin daga yankin Saihat da Sayyid Jafa Alawi daga yankin Safawi dukkaninsu daga lardin Qatif da ke gabashin saudiyya.

Kwamitin kare hakkin bil adama na Saudiyya ya ce babu wani bayani har yazu dangane da dalilan kama su.

Kwamitin ya kara da cewa Sheikh fahami Zaunuddin da kuma Sayyid Jafar Alawi, suna daga cikin malamai masu gudanar da harkoki na addini a yankunan da e cikin lardin Qatif.

Kafin wannan lokacin ma jami’an tsaro na Saudiyya sun kame wani dan kasar a yankin Ihasa.

Wannan mutum mai sun aAli Khalifa, jami’an tsaron Saudiyya a cikin kayan saki sn kai farmai ne kan ofishinsa a inda yake aiki, inda suka kame suka yi awon gaba da shi.

Shi ma dai har yanzu babu wani bayani kan dalilan kama shi da jami’an tsaron suka bayar.

3527104


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha