Kamfanin dillancin labaran kur'ani iqna ya habarta cewa ya nkalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a ranar Laraba ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gudanar da rangadi na sama da sa'oi biyu a wajen baje kolin kayayyaki da makaman kariya na zamani da masana da masu bincike na Ma'aikatar tsaron kasar Iran suka kera da aka gudanar a Husainiyar Imam Khumaini (r.a), wanda yake da tasiri kai tsaye cikin irin karfin da dakarun kasar Iran din suke da shi.
A wajen baje kolin dai an baje kayayyaki da na'urorin kariya na zamani da suke da alaka da makamai masu linzami, na'urorin radar masu hangen nesa, na'urorin kariya da garkuwa, jirage marasa matuki da kuma cibiyoyin sadarwa.
Bangaren farko na kasuwar baje kolin ya kumshi irin na'urorin tsaro da kariya na makamai masu linzami masu cin gajeren zanto, matsakaicin zango da kuma dogon zango.
Haka nan bangare na biyu na kasuwar baje kolin da Jagoran kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran ya kai ziyarar shi ne bangaren nau'oi daban-daban na na'urori na zamani da suke tafiyar da jiragen ruwan yaki na doron ruwa wadanda masana da kwararru na Ma'aikatar tsaron suke tsara da kuma kerawa.
Har ila yau bangare na uku na kasuwar baje kolin shi ne bangaren na'urori daban-daban na nau'oin radar mai hangen nesa na sanya ido. A wannan bangaren jami'an ma'aikatar tsaron sun yi wa Jagoran karin bayani kan ayyukan da aka yi a wajen musamman dangane da na'urar kariyar nan ta Bavar 373. Ita dai wannan na'urar tana karfin aiwatar da ayyuka sama da na'urori makamaniyarta na kasar waje.
Da dai sauran nau'oi daban-daban na nau'rori da makamai na kariya da masanan Iran suka kera su.
Bayan kammala rangadin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya gana da minista, jami'ai da masanan Ma'aikatar tsaro inda ya bayyana karfafa irin karfi na kare kai da kuma mayar da martani a matsayin wani hakki na kasar Iran da babu wanda ya isa ya hana ta. Haka nan kuma yayin da yake bayanin wajibcin ci gaba da bin tafarkin kara karfafa bangaren karfin da ake da shi, Jagoran ya bayyana cewar: A irin wannan duniya da wasu masu tinkaho da karfi, 'yan mulkin marasa komai kashin kyawawan halaye da lamiri na dan'adamtaka suke mulkinta, sannan kuma ba sa jin kunyan kai hari da wuce gona da iri kan kasashe da kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba, karfafa irin karfin kariya da ake da shi wani lamari ne da babu wata matsala cikinsa. Don kuwa wadannan masu takama da karfin matukar dai ba su ji irin karfin da wata kasa take da shi a jikinsu ba, to kuwa ba za su kiyaye tsaronta ba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana rangadin da ya kai wajen baje kolin a matsayin abin faranta rai inda ya ce: Dalilin wannan farin ciki, baya ga ganin irin wannan karfi na kariya da ake da shi wanda ko shakka babu zai kara irin karfin da kasa take da shi, akwai kuma batun ganin dakaru masu ilimi, masana da ma'abota tunani da imani, wanda lalle abin farin ciki da jin dadi ne.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Samuwar irin wadannan mutane da dakaru a fagen kera makamai da nau'orin kariya na kasa, tabbas tamkar wani abu ne mai kimar gaske wanda ba za a iya lissafa shi ba.
Daga nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci sai ya ci gaba da bayanin wajibcin karfafa irin karfin da ake da shi, inda ya ce: A yayin da masu tinkaho da karfi na duniya suka baza komar ikonsu sannan kuma babu wata alama ta rahama a idanuwansu, a fili suke kai hari kan taron aure da asibiti ta hanyar fakewa da batun fada da ta'addanci inda suke kashe daruruwan mutanen da ba su ci ba su sha ba, sannan kuma babu wata cibiya da kungiya da za ta hukunta su, a irin wannan yanayin wajibi ne a karfafa irin karfi na kariya da ake da shi, don masu tinkaho da karfin su ji akwai wata barazana da take fuskantarsu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tabbas mu dai ba mu da wani haddi da kan iyaka a bangaren karfafa irin karfi na kariya da muke da shi, amma bisa tushen akida da addininmu mallakar makaman kare dangi irin su makamai masu guba da makaman nukiliya haramun ne.
Jagoran ya kara da cewa: Haramcin makamai masu guba ya shafi bangaren kai hari ne, to amma babu matsala wajen kara karfi a bangaren kare kai daga hare haren makamai masu guba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Baya ga wadannan kan iyakokin, a sauran fagage kan ba mu da wani kan iyaka wajen karfafa irin karfi na kariya da soji da muke da shi. Ci gaba a wadannan fagage kan ma wani nauyi ne.
Haka nan kuma yayin da yake isharada irin matsayi mai muhimmanci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take dashi hakan nan kuma da wannan yanki na yammacin Asiya bugu da kari kan burin da 'yan mulkin mallaka suke da shi na mallake yankin, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Don tabbatar da tsaro na kasa da kuma makoma, baya ga karfi na kariya, wajibi ne kuma a kara irin karfi na kai hari da mayar da martani da ake da shi.
Har ila yau kuma Jagoran yayi ishara da irin fushin da kasashen 'yan mulkin mallaka suke yi dangane da sayen wasu makamai na kariya da Iran ta yi daga wasu kasashen waje inda ya ce: Wadannan manyan kasashe wadanda suke ikirarin amfani da hankali da kuma adalci, suna magana kan dacewa ko rashin dacewar wasu kasashen wajen mallakan makaman kariya, amma su da kansu babu wata doka da kuke girmamawa.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce gwamnatin Amurka ba ta da wani bakin magana dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana mai cewa: Babu guda daga cikin jam'iyyun Amurka, ba mai mulki yanzu da kuma wacce ta yi mulki a baya ba, da take da dacewa irin ta kyawawan halaye ba. Don kuwa kowace guda daga cikin jam'iyyun biyu ta aikata munanan ayyuka.
Ayatullah Khamenei ya bayyana "samar da kungiyoyin 'yan ta'adda masu hatsarin gaske' a matsayin babban laifin da jam'iyyar da ke mulki a Amurka a halin yanzu ta aikata. Daga nan sai ya ce: Gwamnatin Amurka mai ci yanzu ta kasance tana nuna adawa ta zahiri ga wata kungiyar 'yan ta'addan, sannan kuma tana tsarkake wata kungiyar ta'addancin ta daban, wanda hakan yana nufin fifita siyasa a kan kyawawan halaye.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Gwamnatin Amurkan da ta gabata itace ta haifar da bala'oi da munanan ayyukan da aka yi a Iraki da Afghanistan; ta yadda miliyoyin mutanen da ba su ci ba su sha ba suka rasa rayukansu da kuma kashe dubban masanan kasar Iraki ta hannun kungiyar nan ta 'yan ina ga kisa ta Black Water.
Jagoran ya jaddada cewar: A saboda haka babu guda daga cikin manyan jam'iyyun Amurka guda biyun nan da za a iya fifita ta kan 'yar'uwanta.
Ayatullah Khamenei ya ce: Mu dai muna fuskantar irin wadannan gwamnatoci ne a Amurka, don haka tunanin cewa za a iya magance sabanin da ke tsakaninmu da ita ta hanyar tattaunawa lalle hakan kuskure ne.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Ci gaba da jaddadawar da nake yi kan rashin amfanin tattaunawa da Amurka saboda wannan dalilin ne. Don kuwa tarihi ya tabbatar cewa a yayin tattaunawa Amurkawa maimakon fahimtar juna abin da suka sa gaba shi ne kokarin tilasta manufa da bukatunsu, wanda babban misalin hakan shi ne abubuwan baya-bayan nan da suka faru.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa masana da kwararrun ma'aikatar tsaron na Iran dangane da irin wannan namijin kokari da suke yi.
Kafin jawabin Jagoran, sai da ministan tsaron kasar Iran din Birgediya Janar Husain Dehqan ya gabatar da jawabinsa dangane da irin ayyukan da ma'aikatar take yi a fagen makaman kariya da Iran take bukatarsu.