Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na almanitor cewa, ma’aikatar kula da ahrkokin addini ta kasar Masar ta sana da shirinta na sama da wuta batiri masallatan kasar da nufin rage yawan amfani da wutar lantarki.
Kafin wannan lokacin shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi ya bayyana muhimmancin sama da wasu hanyoyi na rage yawan amfani da wutar lantarki a masallatai, da ruwa gami da iskar gas da ake amfani da su.
Muhammad Yaani shi ne kakakin ma’aikatar wutar lantarki a kasar Masar ya bayyana cewa, yanzu haka sun fara samar da wasu mitoci na musamman da ake yi wa caji domin adana wutar lantarki guda 300 ga masallatai da suke da alaka da ma’aikatar kula da addini, sai kuma wasu 600 na masallatan gari, yayin da kuma aka samar da guda 150 ga majami’oi.
Bayanin ya c yin amfani da wadannan mitoci zai tamaka matuka wajen rage yawan wutar da ake yin amfani da ita a masalatta da kuma majami’oin kasar, wanda kuma zai bayar da damar yin amfani da ita a wasu wuraren.
Yanzu haka dai akwai masallatai dubu 114 a kasar Masar, kimanin dubu 31 na garuruwa ne, sai kimanin dubu 83 kuma na ma’aikatar kula da harkokin addinai ta kasar ne.
Haka nan kuma akwa kimanin majami’oin mabiya addinin kirista guda 3500 a kasar.