Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Kerman ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a nan Tehran inda yayi kakkausar suka ga wadanda suke kiran da a yi kokarin tafiya tare da Amurka.
Ayatullah Kermani ya kara da cewa babu wani abin da Amurka ta ke yi wanda zai amfani Iran face dai abubuwan da za su cutar da ita da kuma al'ummar kasar don haka yayi kiran da a kara himma wajen ciyar da kasar Iran gaba da kuma dogaro da irin karfi na cikin gida da ake da shi.
A wani bangare na hudubar tasa, wanda ya jagoranci sallar Juma'ar na Tehran ya sake jaddada maganganun da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi na wajibcin aiwatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai wanda ya ce hakan ne kawai hanya guda da Iran za ta samu karfaffen yanayi na tattalin arziki da kuma kare kanta daga duk wata barazana ta makiya a wannan bangaren.
Kamar yadda kuma yayi ishara da wajabcin da ke akwai a kan musulmi da su zama cikin fadaka kan makircin da ake kulla musu domin rarraba kansu, inda kuma makiya a halin yanzu za a iya cewa sun samu nasara zuwa wani haddi kan haka, inda abin ban takaici suke amfani da gamnatocin wasu manyan kasashen kasashen larabawa domin aiwatar da wannan manufa ta rarraba kan al’ummar musulmi.