Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin yad alabarai na cibiyar yada al'adun
muslunci cewa, wannan taro dai karamin ofishin jakadancin kasar Iran ne ya
dauki nauyin shirya shi, da zai samu halartar 'yan shi'a na Pakistan, Indiyawa
da kuma na Somalia.
A yayin wannan taro, baya ga karamin jakadan Iran da zai gabatar da jawabi, wasu daga cikin masana na kasar ta Ethiopia ma za su gabatar da jawabinsu a wurin kan muhimmancin wannan rana da matsayinta ta fuskoki da dama.
Tun daga farkon watan muharram ne dai ake gudanar da wannan taro na raya dararen Ashura a ofishin jakadancin kasar Iran da ke Ethiopia, inda ake gudanar da jawabai da kuma yin makoki na juyayin shahadar Imam Hussain (AS) da kuma sauran abubuwan da ake gabatarwa na tunatarwa a yayin taron.