Kamfanin dillancin labaran kur’ani
na iqna ya habarta cewa, Qais Muhammadawi babbn jami’in soji maikula da yankin
Furat ya bayyana cewa, wannan adadi ya hada da masu ziyara na cikin Iraki ne da
kuma wadsanda suka zo daga kasashen ketare.
Haka nan kuma ya kara da cewa adadin wadanda suka yi tafiyar tuwairij ya kai miliyan biyu, kuma tafiyar da suka yi zuwa cikin birnin karbalata kai ta sa’oi uku a jere.
Tafiyar tuwairij dai ana fara ta a lokacin Ashaura baya kiran sallar zuhur, kuma ana faraway daga yankin Kantaratu Salam, ana bi ta hubbaren Abbas (AS) zuwa hubbaren Imam Hussain (AS)