Kamfanin
dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin
sadarwa na yanar gizo na inewsarabia.com cewa, ma’aikatar kula da harkokin
addini ta kasar Morocco ta sanar da cewa, wannan shi ne kari na 12 da za a
gudanar da wannan gasa ta sarki Muhammad na shida a kasar.
Bayanin ma’aikatar kula da harkokin addinin ta kasar Morocco ya kara da cewa, taron gasar zai samu halartar makaranta da mahardata daga kasashen larabawa da na msuulmi da ma sauran kasashen duniya.
Bisa ga wannan rahoto za a bude babban zaman taron ne a cikin watan gobe, a babban masallacin Hassan na 2 da ke birnin kazablanka, daya daga cikin manyan biranan kasar.