Kamfanin dillancin labaran kur’ani
na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na
machahid24.com cewa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki
kan masallatai na Quds, Falah, da kuma Safa a cikin yankin Lisasfah da ke a
gundumar Kazablanka.
A fili take kan cewa duk wadanda suka aikata wannan aika-aika sun yi hakan ne da nufin harzuka musulmi, domin kuwa dukkanin musulmi ba za su ji dadin abin da ak ayi na keta alfarmar masallatai ba.
Baya da keta alfarmar masallatai wadanda wuraren ibada na musulmi, an kuma keta alfarmar kur’ani mai tsarki.
Har yanzu dai ba iya tantance mutanen da suka aikata wannan abu ba, amma dai jami’an tsaro sun ce sun shiga gudanar da bincike kan lamarin, domin gano dukkanin wadanda suka aikata hakan tare da gurfanar da sua gaban kuliya, domin fuskantar sakamakon aikinsu.