IQNA

Ginin Masallaci Mafi Tsada A Cambridge Da Ke Ingila

16:45 - November 03, 2016
Lambar Labari: 3480904
Bnagaren kasa da kasa, musulmi mazauna birnin Cambridge na kasar Birtaniya suna shirin gina wani masallaci mafi tsada a birnin baki daya.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Cambridge cewa, wannan masallaci gininsa zai lakume zunzurutun kudade har pound miliyan 15, wanda zai kasance mai fadi da wuraren ajiye ababen hawa, da wurin sallah da zai dauki mutane dubu.

Haka nan kuma wannan masallaci zai kunshi fili a cikinsa da za aiya shuka kayan ganye da kuma dakin cin abinci, da kuam wuraren tace ruwa wanda ake amfani da sun a zamani, wadanda dukkaninsu hanyoyi ne da za su iya kawo ma masallacin kudin shiga.

Wasu daga cikin musulmi daga jami’ar birnin na Cambridge ne suka gabatar da wannan shawara wadda kuma mahukunra suka amince da ita, inda yanzu haka an fara sayen kekuna dubu 35 domin bayar da haya da nufin fara tattara kudaden aiki.

Babban mai kula da shafin yanar gizo na shirin gina masallaci ya bayyana cewa za aiya ziyatrat shafin ganin irin shirin da suke da shi, shafin kuwa shi ne webcom, wanda dukkanin bayanani da kuma hotuna da aka saka na tsarin yadda masallacin zai kasance duk suna aciki.

Yanzu haka dai akwai kimanin musulmi dubu 7 da suke rayuwa abirnin, kuma suna da masallatai guda 5 da suke amfani da su.

3542987


captcha