Bayan kammala salla daliban sun fito kan titi suna jerin gwano suna yin kira ga sabon shugaban kasar da sauran masu akidar kymar musulmi a kasar da su sake yin nazari.
Daliban sun bukaci Trump da ya zama shuga na dukkanin Amurkawa da suka hada da muslmi da ma wadanda ba msuulmi ba, a kan haka dole ne ya yi adalci a matsayinsa na zababben shugaban Amurka.
Bayan lashe shugaban kasar da ya yi Trump ya yi kalamai masu ban mamaki, inda y ace zai mulki ba tare da nuna kyama ga wani bangare ba saboda banbancin akida ko addini ko launin fata, zai yi aiki tare da dukkanin al'ummar Amurka baki daya.
Tun bayan sanar da lashen shugaban kasa da Trum ya yi musulmin kasar Amurka suna cikin halin damuwa, musamman saboda irin kalaman batuncin da ya yi ta yi a kansu a lokacin yakin neman zabe.