Kamfanin
dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wasu daga cikin tawagar
Iraniyaw amsu ziyarar arbain na Imam Hussain (AS) sun yada zangoa wani tanti na karatun kur’ani mai tsarki a
kan hnyar Najaf zuwa Karbala.
Daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani na kasar Iraki Ibrahim Albadiri ya yi tilawar ayoyin kr’ani mai tsarkia wurin, kafin daga bisani kuma Abu Tahsin Najjar shugaban masu aikin sa kai na yada karatun kur’ani a tattakin arbain ya gabatar da nasihohi.
An daga tutar hubbaren Sayyidah Fatima Ma’asuma (SA) a cikin wannan tanti na hidima ga kur’ani mai tsarki, inda daga bisani aka bayar da kyautar wanann tuta mai labrka ga masu gudanar da hidima a wannan tanti.