Kmfanin
dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin yada
labarai na jaridar daily Sabah cewa, Wata mata musulma mai suna Tunzal Muhammad
Zadah 'yar kasar Azarbaijan yar shekaru 33 da haihuwa,ta rubuta cikakken
kur'ani mai tsarki da hannunta a kan kyallayen alhariri, tare da yin amfani da
tawada da aka hada ta da ruwan zinari da azurfa.
Bayanin ya ci gaba da cewa yana daga cikin ayyuka da aka gudanar masu daukar hankali matuka da suka danganci kur’ania cikin tarihi, kuma wannan kwafin kur’ani ya shiga cikin tarihi.
Wannan mata dai ta dauki shekaru kimani uku a jere tana gudanar da wannan aiki mai babbar kima, wanda kuma cikon ikon Allah ta samu nasarar kammala aikin a cikin wannan shekara.
Da dama daga cikin masana sun nuna mamakinsu matuka dangane da yadda wannan mata ta gudsanar da wannan gagarumin aiki a cikin kankanin lokaci.