IQNA

Tsohuwa 'Yar Shekaro 75 Ta Hardace Kur'ani

22:50 - December 10, 2016
Lambar Labari: 3481020
Bangaren kasa da kasa, wata tsohuwa yar Morocco da ke zaune a Spain yar shekaru 75 da haihuwa ta hardace kur'ani mai tsarki baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Turaikat cewa, Haj Khanom Sa'diyyah yar asalin kasar Morocco da take zaune a kudancin kasar Spain, ta samu nasarar hardace kur'ani mai tsarki.

Wanann tsohuwa yar shekaru 75 da haihuwa, tana fama da matsaloli da suka hada kula da diyarta da ke fama da rashin lafiya, amma duk da hakan ta yi amfani da lokacinta wajen ganin ta hardace kur'ani.

Babban malamin da ke jagorantar salla a masallacin da ke yankin da take rayuwa ya jinjina mata matuka inda ya bayyana cewa, hakia abin da Haj Khanom Sadiyyah ta yi babban abin koyi ga mata da maza baki daya.

Ita dai wannan mata ta kasance mai matukar sha'awar karatun kur'ani, amma kuma ba ta iya samun damar yin hard aba a lokacin rayuwarta ta kuruciya ba, sai bayan da girma ya riske ta, amma duk da haka ta taimakon Allah ta iya cimma burinta.

3552637


captcha