Kafin wannan lokacin dai mahukuntan Masar sun zargi jagororin kungiyar 'yan musulmi da ke zaune a kasar qatar da hannua a cikin lamarin, kasantuwar wanda ya kai harin yana zaune a kasar qatar tun kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Mutane 27 ne suka rasa rayukansu sakamon kai harin, yayin da wasu fiye da 50 suka samu munan raunuka.
Shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi ya sanar makoki na tsawon kwanki uku a fadin kasar, domin nuna alhini kan abin da ya faru.
Tun kafin wannan lokacin dai an kaddamar da hare-hare a kan mabiya addinin kirista, amma wannan shi ne mafi muni, wanda kuma ya girgiza kowa a kasar.
A yau ma wasu daga cikin 'yan kabilar kibtawa sun bukashugaban kasar da ya yi murabus daga kan mukaminsa, bisa abin da suka kira kasa kiyaye rayukansu.
A cikin shekara ta 2011 ne dai 'yan ta'addan suka fara kaddamar da hare-hare a kan al'umma a Masar, tun bayan kifar da gwamnatin Mubarak daga nan kuma yan uwa musulmi suka karba, wanda nan suka kara samun dauriun gindi fiye da kowane lokaci.