IQNA

Taron Raya Makon maulidin Manzon Allah (SAW) A Najaf

16:28 - December 16, 2016
Lambar Labari: 3481041
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na raya makon maulidin mazon Allah (SAW) da Imam Sadiq (AS) a birnin Najaf na kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hula da jama'a na hubbaren Alawi cewa, a ci gaba da tarukan tunawa da zagayowar haihuwar fiyayyen halitta (SAW, an gudanar da taron makon raya al'adun muslunci a Najaf.

Wannan dai yana daga cikin shirye-shiryen da ak egudanarwa a kowace shekara airin wannan lokaci mai albarka, wanda kan mayar da hankali kan muhimamn lamurra da suka shafi al'adu da ilimi na muslunci.

Shirin dai ya kebanci mata ne zalla, kuma aka gudanar da gasa ta rubutu da kuma bayani kan wasu abubuwa da suka shafi mata da kuma gudunmawarsu a cikin addinin muslunci tun daga lokacin manzon har zuwa yau.

Kamar kowace shekara a kan bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a cikin rubutun nasu, a duk lokacin kammala taron wanda ake daukar mako guda ana gudanar da shi.

3554340


captcha