IQNA

Sheikh Na’im Kasem A Tattaunawa Da IQNA:

'Yantar Da Aleppo Ya Rusa Shirin 'Yan Ta'adda

23:46 - December 18, 2016
Lambar Labari: 3481045
Bangaren kasa da kasa, Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana 'yantar da birnin Aleppo daga 'yan ta'adda a matsayin wata babbar nasara, wadda ta kawo karshen mafarkin 'yan ta'adda da masu mara musu baya na kafa wata daular ta'addanci a birnin.

A tattaunawarsa da kamfanin dillancin kur’ani na IQNA ne Sheikh Na'im Kasim ya bayyana hakan ne bayan kammala taron makon hadin kai a birnin Tehran na kasar Iran, inda ya ce ko shakka babu kafa kungiyoyin 'yan ta'adda irin na ISIS da aka cusa musu mummunar akida ta kafirta musulmi, hakan ya bakanta fuskar musulunci a idon duniya, musamman a kasashen turai da sauran kasashen da ba na musulmi ba.

Malamin ya ce kasashen da suke daukar nauyin 'yan ta'addan ISIS wato Amurka, Saudiyya da kuma Isra'ila da wasu 'yan koransu, sun kammala dukkanin shirinsu na mayar da birnin Aleppo wata daular 'yan ta'addan takfiriyya ta biyu bayan Mausil, to amma a cikin ikon Allah shirinsu ya rushe a kan Aleppo baki daya, bayan sun kashe biliyoyin daloli a kan hakan, kamar yadda kuma da yardar Allah shirinsu zai rushe a Mausil.

Haka nan kuma ya yi kira ga sauran malamai da ba su sayar da lamirinsu ga ga dalolin man fetur ba, da su mike tsaye wajen kare martabar addini da ake neman rusawa, su bayyana ma duniya kyawawan dabi'u da kuma sahihiyar koyarwa irin ta manzon Allah, tare da nuna ma duniya cewa akidar takfiriyya da ta'addanci ba su a cikin koyarwar muslunci balantana sunnar manzon Allah da ake fakewa da ita wajen yada wannan mummunar akida.

An dai gudanar da traon makon hadin kai a kasar Iran ne tare da halartar malamai da masana daga kasashen duniya daban-daban fiye da 50, musamman na musulmi, da suka hada da Malaysia, Rasha, Indonesia, Iraki, Lebanon Thailand, Alageriya, Ingila, Amurka, Amustralia, Tunis, China, amsar da sauransu.

3554613


captcha