IQNA

An Kakaba Wa Musulmin Myanmar Harajin Dole

23:12 - January 01, 2017
Lambar Labari: 3481090
Bangaren kasa da kasa, magajin garin birnin Samuna na kasar Myanmar ya kakaba wa musulmi biyan harajin dole a birnin.

Kamfanin dillancin labaran arakan ya bayar da rahoton cewa, dubban daruruwan musulmi da suka kaurace wa muhallansu suka bazu zuwa wasu biranan kasar Myanmar domin tsira da rayukansu suna ci gaba da fuskantar gallazawa.

Garin Samuna da ke arewacin birnin Mongdu na daga cikin garuruwan da musulmi suka fake a cikinsu sakamakon hare-haren da sojoji suka kai kansu tare da ‘yan addinin Buda masu tsatsauran ra’ayi, inda suka kashe musulmin tare da kone musu gidaje da kaddariri a yankunasu da ke cikin lardin Rakhin.

Magajin garin birnin Samuna ya yi barazanar cewa zai sanya sojoji da jami’an tsaro su kori dukkanin musulmin ad suka shigo garin, ko kuma su rika bayar da haraji na wasu kudade masu yawa.

Wannan mataki ya zo sakamakon sallar juma’a da musulmin suka gudanar a cikin wannan makoa wani wurin da aka tsugunnar da su, inda magajin garin ya ce bai amince a rika gudanar da wasu ayyuka makanta hakan ba, sai dai idan za a biya shi harajin da kayyade.

Tun daga bayan kisan gillar da aka yi wa musulmin Rohingya a cikin ‘yan watannin da suka gabata a Myanmar, ya zuwa yanzu dubban daruruwa daga cikinsu ne suka rasa muhallansu.

3558540


captcha