IQNA

Walid Bin Talal Ya Tabbatar Da Cewa Al Saudu Ne Suka Kafa Daesh

23:43 - January 06, 2017
Lambar Labari: 3481106
Bangaren kasa da kasa, Yarima Walid bin Talal biloniya dan gidan sarautar Saud ya tabbatar da cewa masarautar Saudiyyah ce ta kafa ISIS kuma take daukar nauyinta.

Kamfanin dillanicn labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, babbar kotun kasar Saudiyyah ta hana iyalan Walid Bin Talal fita daga kasar da kuma hana taba dukaknin kaddarorinsa da ke kasar.

Wannan mataki dai ya zo bayan wasu bayanai da ya watsa dangane da alakar da ke akwai tsakanin masu mulkin Saudiyya da kuma kungiyar ISIS, inda y ace su ne suak kafa kungiyar kuma suke daukar nauyinta.

Haka nan kuma ya kara da cewa wasu daga cikin kasashen larabawa na yankin teku fasha suna da hannu dumu-dumu a cikin dukkanin ayyukan ta'addancin da wannan kungiya take aikatawa a Syria.

Walid Bin Talal ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada shi da tashar talabijin ta CNN, inda ya ce 'ya'yan gidan Saud da ke rike da madafun iko a Saudiyya a halin yanzu su ne suka kafa ISIS kuma suke kasha biliyoyin daloli wajen daukar nauyinta, ya ce an kafa kungiyar ne a birnin Riyadh fadar mulkin masarautar iyalan gidan saud.

3560059


captcha