IQNA

Sake Bude Masallacin Quebec Na Kasar Canada Bayan Kisan Masallata

19:09 - February 02, 2017
Lambar Labari: 3481194
Bangaren kasa da kasa, Bayan shudewar 'yan kwanaki da kisan gillar da aka yi wa massalata a cikin masallacin Quebec a kasar canada, an sake bude kofofin masallacin ga masallata.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, shafin yada labarai na ibtimes daga kasar Canada ya bayar da rahoton cewa, kwamitin da ke kula da masallacin Quebec a kasar Canada ya sake bude wannan masallaci domin ci gaba da gudanar da ayyukan ibada a cikinsa kamar yadda aka saba.

Muhamamd Lubaidi shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin masallacin, ya sheda wa manema labarai cewa, sun bude masallacin ne domin a ci gaba da gudanar da harkoki da taruka na addini, kuma mika godiyarsa ga dukkanin mutanen kasar ta Canada da suka nuna takaicinsu matuka dangane da abin da aka yi musulmi a wannan masallaci.

Ya kara da cewa yanzu haka akwai sauran abubuwan da suka rage da ba akammala gyara su ba, amma dai hakan ba zai hana aci gaba da gudanr da salla da ayyukana ibada a cikin masallacin ba.

A ranar Lahadi da ta gabata ce wani mutum ya kai farmaki a kan masallacin na Quebec a lokacin da musulmi suke salla, inda ya kashe mutane 6 tare da jikkata wasu.

3569799


captcha