IQNA

20:51 - February 18, 2017
Lambar Labari: 3481241
Bangaren kasa da kasa, wasu majiyoyi a harkar muslunci a Najeriya sun ce gwamnatin jahar Kaduna za ta karbi shekh Ibrahim Zakzaky domin yi masa shari'a a jahar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin shafaqna cewa, wasu majiyoyi a cikin harkar muslunci a Najeriya sun ambata cewa, mahukuntan Najeriya za su mika sheikh Zakzaky ga gwamnatin kaduna domin yi masa shari'a a can.

Wannan yana zuwa ne bayan shudewar wa'adin da kotun tarayya ta bayar da ke umartar mahukuntan na Najeriya da su sake shi a cikin kwanaki arba'in da biyar tare da matarsa da ake tsare da shi tare da ita, tare da biyansa diyya da kuma gina masa wani maimakon gidansa da jami'an tsaro suka rusa.

Majiyoyin sun ce gwamnatin jahar Kaduna na son ta hukunta malamin ne bisa dukkanin ayyukan da harkar muslunci take gudanarwa a cikin jahar Kaduna a cikin fiye da shekaru talatin da suka gabata.

3575340


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: