IQNA

23:38 - February 23, 2017
Lambar Labari: 3481256
Bangaren kasa da kasa, Girtt Wilders dan majalisar dokokin kasar Holland da ya shahara wajen kiyayya da msulmi ya sake yin wasu kamalan batunci a kan addinin mulsunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Girtt Wilders dan majalisar dokokin kasar Holland daga jam’iyyar Freedom Party yana ci gaba da yin amfani da salonsa na nuna kyama ga musulmi da sukar addinin muslunci a matsayin wani babban makamin yakin neman zabe a mazabarsa.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban magoya bayan jam’iyyarsa ya bayyana cewa, addinin mslunci shi ne addini mafi hadari a duniya, domin kuwa yana take hakkoin bil adama tare da bautar da dan adam.

Ya buga misali da kasashen msuulmi, inda yake cewa idan aka yi la’akari da kasashen musulmi yana mai ishara da kasashen larabawa, inda yake cewa za a mutane bas u da ‘yanci, ana take hakkokinsu a matsayinsu na ‘yan adam, sabanin kasashen turai, inda mutum yake da ‘yancin ya yi duk abin da ya ga dama, kuma ya fadi abin da ya ga dama, ba tare da an takura shi ba.

Haka nan kuam ya dauki alkawalin cewa idan har ya sake cin zabe, to zai hana musulmi shiga mazabarsa, kuma zai rufe masallatai da cibiyoyin musulmi da suke a wadannan yankuna, haka nan kuma zai gabatr da daftrin kudiri a gaban mjalaisa domin a hana musulmi shiga cikin kasar Holland baki daya.

A kwanakin baya ne Giett ya kira wasu musulmi ‘yan kasar Morocco mazauna da Kalmar shara, yana mai nufin cin zarafi a gare su da tozarta su.

3577498


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: