IQNA

Taron Kur'ani Na Kasa Da Kasa Mai Taken Sa’id Bin Jubair

23:39 - March 05, 2017
Lambar Labari: 3481285
Bangaren kasa da kasa, a ranar laraba mai zuwa za a fara gudanar da taro kan kur'ani mai tsarki a lardin Wasit na kasar Iraki mai take Said bin Jubair.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, wannan taro za a fara gudanar da shi ne daga ranar Laraba mai zuwa kuma zai ci gaba da gudana har tsawon kwanaki uku.

Taron dai zai samu halartar makaranta kur'ani mai tsarki da kuma masana kan ilmomin kur'ani daga kasashe 20, inda za a gabatar da jawabai da kuma karatu a dukkanin bangarori na harda da kuma kira'a gami da tafsirin kur'ani mai tsarki.

Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce tunawa da wannan bawan Allah wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada ilimin addinin muslunci musamman tafsirin kur'ani mai tsarki daidai da mahangar manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka.

Said Bin Jubair bin Hashim Alasadi, ya kasance daya daga cikin sahabban Imam Sajjad (AS) wanda ya samu ilimi sahihi daga wannan gida mai tsarki, ya kasance mahardacin kur'ani kuma babban mai tafsirin kur'ani mai tsarki bisa ruwayoyin ahlul bait.

A cikin shekara ta 95 bayan hijirar manzon Allah (SAWW) ya yi shahada a hannun Hajjaju bin Yusuf Al-thaqafi, daya daga cikin azzaluman mahukuntan daular Bani Umayyah da suka yi wa iyalan gidan manzo kisan gilla da mabiyansu.

An haifi Said bin Jubair a cikin shekara ta 45 bayan hijira a garin Kufa na Iraki, a lokacin halifanci Imam Ali (A), ya kasance mafi ilimi a tsakanin sauran jama'a a lokacinsa.

3580729


captcha