IQNA

22:49 - March 19, 2017
Lambar Labari: 3481327
Bangaren kasa da kasa, wata gobara ta tashi a kusa dahubbaren Abbas (AS) da ke birnin Karbala mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin Shfaqana cewa, Qaisar Musawi, bababn jami'in kula da ayyukan agajin gagagwa n gundumar Karbala ya bayyana cewa,a daren jiya an samu tashin obara akusa da hubbaren mai tsarki.

Ya ce amma wanann gobara duk kuwa da cewa ta lakume dukiyoyi da ke cikin shaguna a yankin, sai dai bat aba ran mutum ko daya ba a cikin kariyar Allah.

Kasuwar Allawi dai it ace kasuwa mafi jimawa a birnin karbala kuma tana kusa da hubbaren Abbas (AS) inda take da tsoffin shaguna da kum wurare da jama'a suke a jiye kayan kasuwancinsu.

Birnin karbala shi ne birnin da aka yi waki'ar kisan iyalan gidan amnzon Allah a cikinsa a hannun azzaluman sarakunan da suka kwace iko da karfin tuwo daga gidan manzon Allah da iyalansa.

3585247
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: